Shettima: Najeriya ta tsallake muhimmin mataki a sauyin tattalin arzikinta
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa. Shettima ya bayyana hakan ne a New York yayin wata ganawa da ’yan Najeriya mazauna Amurka, a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81. A cewar wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, Shettima ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako. Ya ce ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 55, yayi
