Shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinawa, Christian Saunders, ya yi kira ga Isra’ila da ta sassauta matakan da take ɗauka kan shigar da kayayyaki da kayan aiki zuwa Gaza.

Saunders ya shaida wa BBC cewa kusan dukkanin mutanen da ke Gaza na zaune ne a cikin tantuna, ƙarƙashin buhunan roba ko kuma a wasu gine-ginen da suka ruguje wani ɓangare.

Ya ce matuƙar ba a samu ci gaba wajen sake gina yankin ba, akwai yiwuwar mawuyacin yanayin rayuwa da rashin tsafta su ƙara jefa al’ummar yankin cikin haɗari.

Saunders ya ce ana matuƙar buƙatar wasu kayayyaki, ciki har da sandunan kafa tanti da man fetur, domin taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunansu, sai dai Isra’ila ta hana shigar da wasu daga cikin kayayyakin.

A baya, Isra’ila ta bayyana cewa matakan da take ɗauka kan wasu kayayyaki, da kuma binciken da take yi kafin a shigar da su Gaza, na da nufin hana ƙungiyar Hamas amfani da su wajen ayyukanta.