Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir , ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar tare da naɗa sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya, gabanin zaɓen ƙasar da aka tsara gudanarwa a ranar 22 ga Disamba 2026 .

Matakin ya zo ne bayan da aka yi wa dokokin zaɓe garambawul, inda aka cire wasu sharuɗɗan da suka haɗa da kammala sabon kundin tsarin mulki da gudanar da ƙidayar jama'a kafin gudanar da zaɓe.

A ƙarƙashin matakin, an cire mataimakan shugaban ƙasar, ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati, sannan an rusa majalisar dokokin ƙasa da majalisun jihohi.

Yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 , wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar, ita ce ta samar da tsarin gwamnatin haɗin kan da aka rusa.

Sai dai wasu 'yan adawa da masu sharhi sun nuna damuwa kan matakin, suna cewa zai iya bai wa Shugaba Kiir damar samun iko mai yawa a lokacin shirye-shiryen zaɓen.

A halin yanzu, wasu muhimman abubuwan da yarjejeniyar zaman lafiyar 2018 ta tanada ba su kammala ba, ciki har da haɗa rundunonin sojojin da ke biyayya ga ɓangarorin da suka yi gaba da juna da kuma kammala sabon kundin tsarin mulki.

Ƙungiyar Amnesty International ta ce rusa gwamnatin riƙon ƙwaryar wani muhimmin mataki ne zuwa ga zaɓen farko na ƙasar, amma ta buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar za su iya yin zaɓe da tsayawa takara cikin 'yanci da tsaro.

Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a shekarar 2011 , amma zaɓen ƙasa na farko tun bayan samun 'yancin kan ya sha jinkiri sau da dama.