AMMASCO RADIO NEWSROOM

Lafiya

Rahoton ICRC ya nuna ƙaruwar matsalar ƙarancin abinci a Najeriya

Hukumar agaji ta ƙasa da ƙasa, ICRC, ta ce matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta ƙaru a wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya, inda adadin mutanen da ke fama da ita ya tashi daga kusan 17,000 zuwa 20,000, bisa bayanan da aka tattara daga cibiyoyin lafiya.

rundunar yan sanda a jihar cross river ta kaddamar da bincike kan likitan Bogi daya yi wa wani dattijo aiki a 'yayan marainansa

Yan sanda a jihar cross river sun cafke wani mutuum da ake zargi likitan bogi ne da ya yiwa wani dattijo mai shekaru 60 aikin ‘ya’yan maraina a garin Ekori dake karamar hukumar Yakurr din jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar Sunday Eitokpah ya sanyawa hannu, aka kuma rabawa manema labarai a garin calaba babban birnin jihar. Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a wani asibiti mai zaman kansa dake garin na Ekori, bayan jikin mutumin da aka yiwa aikin wanda aka fi sani da Ukpan ya tsananta kwanani kadan bayan anyi masa aikin. Kakakin rundunar Eitokpah, ya ce a

NCDC tace jihohi 8 ne ke ɗauke da kashi 98 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar mashako a Najeriya

Hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta fitar da wata sanarwar gargaɗi game da yaɗuwar cutar mashaƙo ta Diphtheria a ƙasar, inda ta bayyana damuwa kan yadda cutar ke ci gaba da barazana ga lafiyar al'umma. Babban abin da ya fi tayar da hankali a cikin rahoton shi ne cewa, kusan kashi 68 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ba su taɓa karɓar allurar rigakafi ba. Wannan babban gibi na rashin rigakafi yana nuna yadda cutar ke samun ƙofar shiga cikin sauƙi tsakanin al'ummomin da ba su da kariya. Hukumomi sun jaddada cewa rashin yin rigakafin shi ne babban makamin da

Karamar Hukumar Funtua ce ke kan gaba a yawan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashako a Jihar Katsina

Karamar Hukumar Funtua ce ke kan gaba a yawan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashako a Jihar Katsina, yayin da rahotannin cutar suka fito daga ƙananan hukumomi 29. Wannan na cikin sanarwar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Katsina ta fitar bayan taron manema labarai da aka gudanar. Sanarwar ta bayyana cewa, bayanan da aka tattara zuwa ranar 28 ga Agustan da muke bankwana da shi sun nuna Funtua ce ke da rahotannin da suka fi yawa, sai Kankia, Bakori, Katsina, Mashi da Daura. Mukaddashiyar Shugabar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dr. Shaima’u Kabir Abba, t

Kungiyar likitoci ta kasa ta bayyana fargabar ficewar wasu dalibanta dake daf da kammala karatunsu zuwa kasashen waje

Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa wasu daliban likitanci na fara shirin barin Najeriya zuwa kasar waje tun kafin su kammala karatunsu, sakamakon rashin kyakkyawan yanayin aiki da makoma a fannin lafiya. Shugaban NMA, Farfesa Afekhide Omoti, ya ce wasu daliban na fara rubuta jarabawar cancantar aiki a kasashen waje tun lokacin koyon aikin likitanci, domin su samu damar yin hijira bayan sun kammala rajista. Omoti ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta inganta albashi, tsaro, kayan aiki da jin dadin likitoci domin dakile yawan barin kasar da kwararrun ma’aikatan lafiya ke yi. Sh

Najeriya Za Ta Ƙarfafa Ɗaukar Jini

Najeriya na shirin ƙarfafa tsarin ɗaukar da jini, yayin da masu ruwa da tsaki ke nazarin wata sabuwar Manufar Ƙasa kan Jini da aka yi wa kwaskwarima, da nufin tabbatar da samar da jini mai aminci, ɗorewa kuma a ko da yaushe ga ’yan ƙasar. Hukumar Kula da Ayyukan Jini ta Ƙasa, National Blood Service Agency , ta ce sake duba manufar ya zama dole domin magance sabbin ƙalubalen da ake fuskanta wajen tattara jini, sarrafa shi, adanawa da rarrabawa. Hukumar ta kuma ce matakin zai taimaka wajen inganta ƙa’idoji da matakan aiki a cibiyoyin ba da sabis na jini a faɗin ƙasar. Daraktan-Janar na Hukumar,

EBOLA TA BARAZANA A KWANGO, YARA 180 SUN RASA IYAYENSU

Wani sabon rahoto daga ƙungiyar Save the Children ya ce aƙalla yara 180 ne suka rasa iyayensu biyu ko kuma waɗanda ke kula da su sakamakon barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. Rahoton ya ce adadin ya kai kusan yara biyu da ke rasa iyayensu ko masu kula da su a kowace rana tun bayan da aka ayyana barkewar cutar a ranar 15 ga watan Mayun 2026. Hukumomin lardin Ituri , wanda shi ne cibiyar barkewar cutar, sun ce yara 180 da suka rasa iyayensu sun ƙunshi yara maza 90 da mata 90. Yawancinsu yanzu suna hannun ‘yan uwa ko kuma cibiyoyin kula da yara na gwamnati. Haka kuma, wasu yar

Za a dawo cigaba da gudanar da shirin rigakafin cizon sauro ranar Laraba, 12 ga Agusta 2026 bayan Rahoton Kwamitin bincike da gwamnatin kano ta nada

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara ƙarfafa sa-ido kan tsarin gudanar da shirin rigakafin maganin cizon sauro na Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) na shekarar 2026, bayan kammala wani cikakken bita kan matakan gudanar da shirin, takardun bayanai da kuma tsarin ma’aikatan da za su aiwatar da shi a faɗin jihar. Wannan na cikin wata Sanarwa mai dauke da sa hannun jami'ar yada labarai ta hukumar Lafiya a matakin farko Sa'adatu Suleiman A cewar sanarwar, mataki ya biyo bayan kafa wani kwamitin bincike da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya yi a ranar Laraba, 5 ga Agusta 2026, domin gudanar da bincik

Gwamnatin Jihar Kano Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Inganta Lafiyar Mata Masu Juna Biyu da Ƙananan Yara

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf , ta ci gaba da nuna ƙuduri wajen inganta harkokin lafiya, musamman ta fuskar kula da mata masu juna biyu da ƙananan yara a faɗin jihar. Tun bayan hawan wannan gwamnati kan mulki, Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta samar da kayayyakin kula da mata masu juna biyu, waɗanda ake rabawa a ƙarshen kowane wata zuwa manyan asibitocin gwamnati da ke sassa daban-daban na jihar. An samar da waɗannan kayayyaki ne domin ƙarfafa ayyukan kula da mata masu juna biyu, musamman waɗanda ke b

Gwamnatin Kano ta dakatar dukan aiyukan bada rigakafin zazzabin cizon sauro

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da dakatar da dukkan ayyukan Shirin Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro a faɗin jihar nan take, domin tabbatar da gaskiya, riƙon da ingancin yadda ake aiwatar da aikin. Hakan na cikin wata Sanarwa da mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano Nabilisi Abubakar Kofar Na'Isa ya sanyawa hannu. Matakin ya biyo bayan Rahoton babban kwamitin bincike da aka ba alhakin gudanar da cikakken nazari kan yadda aka tsara shirin, da yadda aka rarraba magunguna da kuma yadda aka aiwatar da ayyukan SMC a Jihar Kano. A cewar wata sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta

Hana yara shan sukari na inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu

Wani sabon bincike ya nuna cewa rage yawan shan sukari ga yara tun daga haihuwa zuwa shekaru biyu na iya taimakawa wajen kare lafiyar ƙwaƙwalwa har zuwa tsawon shekaru masu yawa. Binciken, wanda masu bincike daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Hong Kong suka gudanar, ya yi nazarin tasirin ƙarancin sukari da aka samu a Birtaniya bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen da suka taso a lokacin da ake taƙaita amfani da sukari a lokacin ƙuruciyarsu sun kasance da ƙananan yiwuwar kamuwa da cutar mantuwa (dementia) da kusan kashi 23 cikin ɗari , idan aka kwatanta da waɗanda s

Sama da mutane 55475 ne suka kamu da cutar amai da gudawa, cikin watanni shida a Jihar kano

Sama da mutane 55475 ne suka kamu da cutar amai da gudawa, cikin watanni shida a Jihar kano Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema Labarai, Kan ranar wayar da kai Kan muhimmancin ruwan gishiri da siga a jikin Dan Adam. Dr Abubakar ya Kara da cewa cikin watanni shida Gwamnantin Kano ta gano sama da mutane 55574 dake sukayi Sama da cutar amai da gudawa, kuma tuni Gwamnati ta dauki matakan gaggawa na samar magunguna ciki har da ruwan gishiri da suga dan kare yara daga mutuwa bisa karancin ruwa a jikinsu. Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dr. Abuba

Gwamnatin kano ta jaddada kudurin hukumar KHETFUN na inganta asibitocin jihar cike da gaskiya da rikon amana wajen kashe kudin hukumar.

Gwamnatin kano ta jaddada kudurin hukumar KHETFUN na inganta asibitocin jihar cike da gaskiya da rikon amana wajen kashe kudin hukumar. Babbar Sakatariyar hukumar ta Kano State Health Trust Fund (KHETFUND), Dakta Fatima Usman Zahraddeen ce bayyana hakan, yayin wata ziyarar tantance ayyukan da aka aiwatar bayan bayar da tallafi a Babban Asibitin Gwarzo, inda aka duba yadda aka aiwatar da ayyukan da darajarsu ta kai Naira miliyan 42,397,000. A yayin ziyarar, Babbar Sakatariyar hukumar, wadda Daraktan Ayyuka na Dakta Lawan Adamu ya wakilta, ta tabbatar da cewa an kammala ayyukan da suka haɗa da s