Aƙalla mutum 14 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon wani harin jirgi marar matuƙi, drone, da rundunar sojin Habasha ta kai a kudancin yankin Tigray.
Gidan talabijin na Dimtse-Woyane da ke yankin ne ya ruwaito hakan, yana ambaton Magajin Garin Alamata, Moges Shiferaw.
A cewarsa, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Talata, 22 ga Satumba 2026, inda aka kai hare-haren drone guda 20 tare da wani hari guda daga jirgin yaƙin soji a garin Alamata da kewayensa.
Moges ya ce hare-haren sun shafi fararen hula da ke kan hanyarsu zuwa kasuwannin da ke kusa, sannan sun lalata gine-ginen makarantu biyu.
Kafafen yaɗa labarai na yankin sun kuma ruwaito wani harin drone daban a gundumar Tahitay Adiabo da ke arewa maso yammacin Tigray. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko harin ya haddasa asarar rayuka ko jikkata ba.
Sashen BBC na harshen Tigrigna ya ce yana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da rahotannin hare-haren tare da hukumomin yankin da kuma majiyoyin cikin gida.
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da ake ƙara fargabar yiwuwar sake barkewar cikakken yaƙi tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da ƙungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) .
A cikin makonnin baya-bayan nan, rahotanni sun ce sojojin gwamnatin tarayyar Habasha sun ƙara yawan hare-haren sama a wasu sassan yankin Tigray.
