Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke gudanar da ayyuka a Arewa maso Gabas sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 1,106 cikin shekara guda.

Rundunar ta kuma ce ta ƙwato makamai sama da 475 , harsasai fiye da 24,000 , tare da lalata bama-bamai 295 da aka ƙera a cikin gida, waɗanda aka fi sani da IED.

An bayyana waɗannan alkaluma ne yayin bikin miƙa ragamar jagorancin Rundunar Operation Hadin Kai daga Manjo Janar Abdulsalam Abubakar zuwa sabon kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose, a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ranar Talata.

An kama waɗanda ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda

Manjo Janar Abubakar, kwamandan da ya bar aiki, ya ce jami’an tsaro sun kama mutum 758 da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda wajen safarar makamai da sauran kayan aiki.

Ya kuma ce mayaƙan JAS da ISWAP 969 , tare da iyalansu, sun miƙa wuya cikin shekara guda, yayin da aka ceto fararen hula 638 daga hannun ’yan ta’adda.

A cewarsa, ayyukan sojojin sun kuma taimaka wajen mayar da iyalai sama da 7,000 da suka rasa matsugunansu zuwa garuruwansu a Jihar Borno.

An sake buɗe kasuwanni da makarantu

Rundunar ta ce an sake buɗe kasuwanni da hanyoyin kasuwanci a wasu yankunan da lamarin tsaro ya shafa.

Haka kuma, an dawo da shirin horas da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a Maiduguri bayan shafe sama da shekaru 13, yayin da aka sake gudanar da jarrabawar WAEC da NECO a wasu yankuna da suka haɗa da Banki da Gwoza.

Sojojin sun kuma ce sun ƙwato kusan Naira miliyan 300 da ake zargin suna da alaƙa da masu ɗaukar nauyin ’yan ta’adda.

Bugu da ƙari, ayyukan rundunar sun taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya sama da 3,000 daga Kamaru.

Sabon kwamandan ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙi da ta’addanci

A nasa ɓangaren, sabon kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya yi alƙawarin ƙarfafa nasarorin da aka samu tare da ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki a Arewa maso Gabas.

Ajose, wanda ya taɓa riƙe wasu muƙamai a Jihar Borno, ya ce zai ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar, ƙungiyoyin agaji, rundunar haɗin gwiwa ta farar hula, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da ta’addanci a yankin.