Fadar Shugaban Ƙasar Amurka ta White House ta ƙaddamar da wata tashar talabijin ta yanar gizo mai suna “Trump TV: The Essentials Station” , bayan da wasu manyan kafafen yaɗa labarai suka dakatar da ɗaukar hotunan ayyukan Shugaba Donald Trump daga White House.
Matakin ya zo ne bayan gwamnatin Trump ta hana kafafen yaɗa labarai na CNN, MS NOW da Politico samun damar shiga White House, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin gwamnatin da wasu kafafen yaɗa labarai.
Trump ya zargi waɗannan kafafen da yada abin da ya kira “labaran ƙarya”, yayin da gwamnatin ta ce damar shiga White House gata ce ba haƙƙi ba.
Bayan dakatar da kafafen guda uku, manyan tashoshin talabijin da suka haɗa da ABC, CBS, Fox News da NBC sun dakatar da ɗaukar wasu shirye-shiryen talabijin na shugaban ƙasar, ciki har da ayyukan da ake ɗauka a matsayin ɓangare na tsarin haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai na White House.
Sabuwar tashar Trump TV tana watsa jawabai da wasu muhimman abubuwan da suka shafi ayyukan gwamnatin Trump. Rahotanni sun ce ba a bayyana cikakken tsarin yadda tashar za ta gudanar da watsa shirye-shiryen kai tsaye ba.
A halin da ake ciki, CNN, MS NOW da Politico sun shigar da ƙara a kotun tarayya kan matakin gwamnatin, suna zargin cewa an tauye musu haƙƙin da Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya tanada na ‘yancin yaɗa labarai.
