Kwamitin Manufofin Kuɗi na Babban Bankin Najeriya, CBN, ya rage Ma’aunin Kuɗin Ruwa na Manufofin Kuɗi (MPR) daga kashi 26.5 zuwa kashi 23 cikin 100.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya sanar da matakin ranar Talata, bayan kammala taron kwamitin karo na 307 da aka gudanar a Abuja tsakanin ranar 21 zuwa 22 ga Satumba 2026.

Ragewar da maki 350 ya biyo bayan tarurruka biyu da kwamitin ya gudanar a watan Mayu da Yuli, inda ya bar kuɗin ruwan a kashi 26.5 cikin 100. A watan Fabrairu kuma, CBN ya rage shi da maki 50 daga kashi 27 zuwa 26.5 cikin 100.

Sai dai CBN ya bayyana cewa matakin ba wai yana nufin sauya manufofin takaita kuɗaɗe ba ne, illa dai wani gyaran tsarin gudanar da manufofin kuɗi ne domin inganta yadda kuɗin ruwa ke tasiri a kasuwar kuɗi da kuma dawo da MPR a matsayin babban ma’aunin manufofin kuɗi.

Matakin ya zo ne yayin da ake samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya. Sabon rahoton Ma’aunin Farashin Kayayyaki na Hukumar Kididdiga ta Ƙasa, NBS, ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 15.39 cikin 100 a watan Agustan 2026 , daga kashi 15.43 cikin 100 a watan Yuli.

Kwamitin MPC ya kuma rage iyakar tsarin Standing Facilities Corridor zuwa +50/-300 maki a kusa da MPR, yayin da ya bar adadin ajiyar kuɗin bankunan kasuwanci, CRR, a kashi 45 cikin 100.

CBN ya ce zai ci gaba da duba tasirin sabon tsarin tare da tabbatar da cewa matakan da zai ɗauka nan gaba za su dogara da sabbin bayanan tattalin arziki.