Hukumomin Najeriya sun ƙara tsaurara matakan tsaro tare da ƙara sanya ido a sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), makarantu da wuraren ibada, sakamakon bayanan sirri da ke nuni da yiwuwar kai hare-haren ’yan bindiga da ƙungiyoyin ’yan ta’adda a sassan ƙasar.
A wata sanarwa da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta aika wa rundunoninta a faɗin ƙasar, ta yi gargaɗin samun ƙaruwar haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin ’yan ta’adda da masu aikata manyan laifuka domin kai hare-haren haɗin gwiwa.
Rundunar ta ce ana zargin shirin hare-haren na iya daidaituwa da lokacin da ɗalibai ke komawa makaranta domin zangon karatu na 2026/2027.
Ana zargin zirga-zirgar mahara a jihohi
A cewar ’yan sandan, bayanan sirri sun nuna yadda wasu gungun mahara ke zirga-zirga daga Jihar Katsina zuwa Kaduna, sannan zuwa Filato.
Rahotannin sun kuma yi gargaɗin cewa mayaƙan da ake zargi da kasancewa na ƙungiyar ISWAP da wasu abokan hulɗarsu na cikin gida na gudanar da bincike da leƙen asiri kan wuraren da ake ganin za su iya kai wa hari.
Gwamnatocin jihohi daban-daban, ciki har da waɗanda ke fuskantar matsalolin tsaro, sun ɗauki matakan kariya tare da shiga shirin ko-ta-kwana domin dakile duk wata barazana.
An cafke mutane biyar a Oyo
A Jihar Oyo kuwa, jami’an tsaro sun cafke mutane biyar da ake zargi da hannu wajen kai hari kan wani sansanin sojoji da ke wajen birnin jihar.
Rahotanni sun ce wasu mahara sun kai hari sansanin sojojin Operation Burst da ke kan hanyar Igbeti zuwa Igboho, a yankin ƙananan hukumomin Oorelope da Olorunsogo.
Maharan sun ƙona motar sintirin jami’an tsaro tare da lalata wani ɓangare na ginin sansanin.
Sai dai rahotannin sun ce babu wanda ya mutu ko ya samu rauni a harin, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a harin.
An yi gargaɗin shirin kafa sansanoni a Osun
Wannan sabon gargaɗin ya zo kwana guda bayan jami’an tsaro a Jihar Oyo sun fitar da bayanan sirri kan wani shiri da ake zargin mayaka na yi na kafa sansanoni a Jihar Osun, da nufin kawo cikas ga zaɓen 2027.
Hukumomin tsaro sun ce suna ci gaba da tattara bayanan sirri tare da ƙarfafa matakan tsaro domin kare makarantu, wuraren ibada, sansanonin NYSC da sauran wuraren da ake ganin za su iya zama wuraren kai hari.
