Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da gano wani jirgi maras matuƙi , wato drone , da ake zargin masu aikata laifuka ne ke amfani da shi.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya ce jami’an rundunar sun gano jirgin ne yayin wani samame da suka kai a iyakokin jihar.

Ya ce jami’an sun ci karo da jirgin ne a wani daji da ke Tarau, a ƙaramar hukumar Bebeji .

A wani ci gaba kuma, rundunar ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa .

CSP Kiyawa ya ce wanda ake zargin mai shekaru 35 ne, mazaunin Kunkumi a ƙaramar hukumar Maƙarfi ta jihar Kaduna , kuma ana zarginsa da kasancewa mamba a wata ƙungiyar masu aikata miyagun laifuka da ke da hannu wajen garkuwa da mutane, fashi da makami da satar shanu a Kano, Katsina da Kaduna.

Ya ce bincike ya kai ga gano wani mutum da ke zaune a Kwanar Ɗangora a Kano , wanda ake zargin yana gayyatar wanda ake zargin mai garkuwa da mutanen domin gudanar da ayyukan laifuka tare.

A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa hannu a wasu ayyukan garkuwa da mutane, ciki har da sace wata mata da aka biya kuɗin fansa naira miliyan 20 kafin a sake ta.

Haka kuma, an ce sun taɓa sace wani mutum a Gwarzo , inda suka kai shi jihar Kaduna, kuma suka riƙe shi har sai da iyalansa suka biya kuɗin fansa.

Kakakin rundunar ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Ya kuma ce kwararru na ci gaba da nazarin jirgin maras matuƙin da aka gano domin gano irin bayanan da ke cikinsa da kuma abin da ake amfani da shi wajen yi .