Aƙalla mutum 11 ne suka jikkata sakamakon harbin bindiga da wani mahari ya yi a wajen wata makarantar sakandare a jihar Manisa da ke yammacin Turkiyya.

Rahotanni sun ce maharin ya buɗe wuta a kusa da makarantar kafin daga bisani ya tsere daga wurin.

Sai dai ofishin gwamnan jihar Manisa ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin.

Kafafen yaɗa labaran Turkiyya sun ruwaito cewa biyu daga cikin mutanen da aka kai asibiti suna cikin mawuyacin hali.

Wasu bidiyoyi da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna wani mutum dauke da bindiga a kusa da makarantar, sannan wani bidiyon ya nuna shi yana gudu daga wurin yayin da yake ɗauke da makamin.

Har yanzu hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka kai harin ba.

Wasu kafafen yaɗa labaran Turkiyya sun ce wanda ake zargin ɗalibi ne mai shekaru 15, sai dai hukumomi ba su tabbatar da wannan bayanin ba.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Ilimi ta Turkiyya ta bayyana cewa lamarin ya jefa ƙasar, musamman ɓangaren ilimi, cikin alhini.

Ma’aikatar ta ce ta tura jami’anta zuwa Manisa domin gudanar da bincike kan harin.