Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin mutum 10 domin gudanar da bincike kan mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a jihar Neja.

Mutanen sun kasance masu haƙar ma’adanai, kuma ana zarginsu da gudanar da aikin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya ƙaddamar da kwamitin a Abuja a yau, bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Babban Daraktan Hukumar DSS, Jonathan Kure, yayin da tsohon babban daraktan makarantar horas da aikin lauya, Farfesa Isa Hayatu, zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da AIG Hosea Hassan Karma mai ritaya; Farfesa Olayinka Buhari, tsohon babban likitan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin; wakilin Masarautar Minna; da wakilin gwamnatin jihar Neja.

Haka kuma, kwamitin ya ƙunshi Alhaji Liman Sulaiman, Sakataren Ƙungiyar Masu Haƙar Ma’adanai ta Ƙasa, da lauya kuma ɗan fafutuka, Deji Adeyanju.

Masu haƙar ma’adanai 37 ɗin sun rasu ne a ranar Alhamis yayin da suke tsare a hannun jami’an NSCDC.

Zuwa yanzu, hukumomi ba su bayyana a hukumance musabbabin mutuwar mutanen ba. Gwamnatin Tarayya ta ce kwamitin zai gudanar da bincike domin gano abin da ya faru da kuma gabatar da rahotonsa ga hukumomin da abin ya shafa.