Aƙalla mutum biyar sun mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace sakamakon wata ƙaƙƙarfar guguwa da ta afkawa gabashin gabar tekun Japan.
Guguwar ta kuma haddasa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, wanda aka ce ba a taɓa samun irinsa ba tsawon lokaci a wasu yankunan da ke kewaye da babban birnin ƙasar, Tokyo.
Ruwan saman ya kuma haddasa katsewar wutar lantarki, lamarin da ya jefa dubban gidaje cikin duhu.
Jami’an hukumar kula da yanayi ta Japan sun buƙaci jama’a da su ci gaba da taka-tsantsan tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana saboda barazanar ƙarin ruwan sama da ambaliyar ruwa.
Guguwar ta kuma tilasta soke wani babban baje kolin wasannin bidiyo da ake gudanarwa a Tokyo, wanda na daga cikin manyan tarukan irin sa a duniya.
Haka kuma, an soke tashin da saukar ɗaruruwan jiragen sama, yayin da aka dakatar da wasu ayyukan sufurin jiragen ƙasa sakamakon mummunan yanayin da guguwar ta haifar.
