Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a Najeriya a halin yanzu.
Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai da aka gudanar domin yin tsokaci kan kwanaki 100 da ya fara a matsayin ministan.
Tegbe ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama a ƙarshen makon da ya gabata, sakamakon rahotannin da suka yaɗu cewa gwamnatin tarayya na shirin ƙara kuɗin wutar lantarki. Ya ce waɗannan rahotanni ba su dace da matakin da gwamnati ke shirin ɗauka ba.
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fi mayar da hankali wajen inganta samar da wutar lantarki da daidaita harkokin ɓangaren makamashi , maimakon ƙara wa masu amfani da wutar ƙarin kuɗaɗe.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin samar da wasu hanyoyin makamashi, ciki har da makamashin hasken rana, tare da gudanar da cikakken bincike kan tsarin samar da lantarki a faɗin ƙasar domin gano matsalolin da ke kawo cikas da kuma magance su.
Tegbe ya ce a cikin kwanaki 100 da ya yi a ofis, an samu wasu ci gaba a ɓangaren wutar lantarki, ciki har da ƙarin ƙarfin samar da wuta da kuma shigar da sabbin mitoci. Ya ce samar da wutar lantarki ya kai kololuwar megawatt 5,330 a watan Agusta da Satumba.
Sai dai ministan ya amince cewa har yanzu miliyoyin ‘yan Najeriya ba sa samun ingantacciyar wutar lantarki a kai a kai, yana mai cewa gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa ci gaban da aka samu ya isa ga masu amfani da wuta a sassa daban-daban na ƙasar.
