Birtaniya ta amince da tura wani jirgin soji na RAF Voyager domin taimaka wa Saudiyya wajen ƙara wa jiragen yaƙinta mai a sararin samaniya, yayin da take fuskantar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa daga ‘yan Houthi na Yemen.

Jirgin zai yi aiki ne daga sansanin sojin saman Birtaniya na RAF Akrotiri da ke Cyprus , kuma ana sa ran zai fara aikin cikin ƴan kwanaki. Aikin na wucin gadi ne, inda ake sa ran zai ɗauki makonni.

Ministan Tsaron Birtaniya, Luke Pollard, ya ce matakin ya biyo bayan buƙatar da Saudiyya ta gabatar, kuma taimakon zai kasance ne domin ayyukan kare kai kawai , ba wai taimaka wa hare-haren da ake kai wa ‘yan Houthi a Yemen ba.

Jirgin RAF Voyager na ba da damar ƙara wa jiragen yaƙi mai yayin da suke cikin sararin samaniya, abin da ke ba su damar ci gaba da shawagi na tsawon lokaci tare da mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Gwamnatin Birtaniya ta ce matakin wani ɓangare ne na tallafin tsaron da take bai wa Saudiyya, wanda ya haɗa da kayan kariyar sararin samaniya da jami’an Birtaniya da ke taimakawa wajen kare ƙasar daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

A 'yan kwanakin nan, ‘yan Houthi sun yi ikirarin kai hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami zuwa Riyadh da wasu cibiyoyin makamashi da ke gabar Bahar Maliya.

Birtaniya ta ce tana ɗaukar matakin ne domin taimakawa wajen kare Saudiyya da kuma rage yiwuwar ƙara tsanantar rikicin yankin.