Kafin nadin nata, Barr. Hafsat Kutama ta kasance Sakatariya kuma Mai Ba da Shawara ta fuskar Shari’a ga hukumar karbar korafe-korafe ta jihar kano tun a watan Agustan 2025.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin mukaddashiyar shugabar Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC).

Nadin nata ya biyo bayan rahotannin cewa Saidu Yahaya, wanda ke jagorantar hukumar tun bayan karewar wa’adin tsohon shugabanta, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi murabus daga mukaminsa.

A baya, Gwamna Abba Yusuf ya nuna damuwa kan raguwar ayyukan hukumar bayan ficewar Muhuyi Magaji, inda ya ce hukumar ta rasa karfin da za ta iya gudanar da ayyukan yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.