Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sake tarwatsa wani dakin gwaje-gwajen sarrafa methamphetamine a wani daji a Jihar Oyo, tare da cafke wani ɗan ƙasar Mexico da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Legas.
Shugaban NDLEA, Birgediya-Janar Buba Marwa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran hukumar, Femi Babafemi, ya fitar.
Marwa ya ce samamen na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin hukumar na dakile samarwa da safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya, musamman wuraren da ake sarrafa su a asirce.
Ya ce jami’an hukumar sun gano wata masana’antar da aka ɓoye a cikin wani daji a ƙauyen Tapa, da ke ƙaramar Hukumar Ibarapa ta Arewa a Jihar Oyo.
A cewarsa, gwaje-gwajen da aka gudanar kan abubuwan da aka samu a wurin sun tabbatar da kasancewar sinadarin methamphetamine da aka sarrafa.
Shugaban hukumar ya ce samamen ya kuma sake bayyana yadda wasu ’yan Najeriya da kuma ’yan ƙasashen waje ke kafa wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi a sassan ƙasar.
An cafke ɗan Mexico a Legas
A wani samame kuma, jami’an NDLEA sun cafke wani ɗan ƙasar Mexico da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, yayin da yake ƙoƙarin barin Najeriya ta filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.
Marwa ya ce wannan nasarar ta biyo bayan binciken kwakwaf da hukumar ta gudanar na tsawon watanni kan wata babbar ƙungiyar masu aikata laifuka.
Ya ce binciken ya biyo bayan gano wasu dakunan gwaje-gwajen sarrafa miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na Najeriya, lamarin da ya sa hukumar ta ƙara zurfafa bincike kan hanyoyin samarwa da safarar miyagun ƙwayoyin.
