Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Zamfara (ZITDA) ta samu lambar yabo daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) bisa ƙoƙarinta na bunƙasa fasahar zamani da inganta shugabancin hukumomi a matakin jiha.
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya kusanci dala 110 kan kowace ganga, a karon farko tun daga watan Mayun 2026, sakamakon fargabar ƙarin tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya da kada ta dawo da tsarin tallafin man fetur, inda ya buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage tasirin hauhawar farashin makamashi.
Matatar man Dangote ta bude sayar da hannayen-jarinta na farko ga jama'a, lamarin da zai bai wa masu zuba jari damar mallakar wani kaso a matatar mai mafi girma a Afirka.
An kaddamar da siyan zuba hannayen-jarin yau Litinin a hukumance awani biki da za a gudanar a zauren hannun-jari na Kasuwar Hannun-Jari ta Nijeriya da ke Jihar Legas.
Matakin zai bai wa jama'a damar mallakar hannun-jari a babban matatar mai ta Afirka wanda kuma ke zama daya daga cikin manyan masana'antu masu matukar muhimmanci a duniya.
Kazalika ana sa ran hannayen jarin matatar zai tara kusan Naira tiriliyan 2.15, adadin da
Jaridar Financial Times ta ruwaito cewa an sake kai hari kan wasu cibiyoyin kamfanin mai na Saudiyya, Saudi Aramco, da ke birnin Jizan a ranar Litinin. Rahoton ya ce harin ya faru ne kusan wata guda bayan wani hari da ya taɓa ayyukan matatar man kamfanin da ke Jizan, yayin da ake ci gaba da tantance girman ɓarnar da sabon harin ya haddasa. Jizan, da ke kusa da iyakar Saudiyya da Yemen, na daga cikin wuraren da hare-hare suka fi kai wa a cikin rikicin yankin. Matatar man Jizan na da ƙarfin tace kusan ganga 400,000 na ɗanyen mai a kowace rana. Babban jami'in Aramco, Amin Nasser, ya ce hare-haren
Farashin man fetur a Jamus ya kai matsayi mafi girma a tarihi, biyo bayan sake barkewar yaƙin Iran, a cewar Ƙungiyar Masu Motoci ta Jamus, ADAC. Ƙungiyar ta ce matsakaicin farashin litar man fetur mai nau'in E10 a faɗin ƙasar ya ƙaru zuwa Yuro 2 da centi 21 a ranar Laraba. Wannan farashin ya zarce tsohon tarihi na Yuro 2 da centi 20 , wanda aka taɓa samu a watan Maris na shekarar 2022. ADAC ta ce baya ga tasirin rikicin Iran, ƙarancin ruwa a kogin Rhine ya kuma taimaka wajen ƙara tsadar man fetur, sakamakon ƙarin kuɗin da ake kashewa wajen jigilar man fetur da sauran kayayyaki. Kogin Rhine na
‘Yan kasuwar man fetur da masu shigo da shi sun yi watsi da rahoton cewa matatar Dangote na shirin dakatar da sayar da fetur ga ‘yan kasuwar da ke shigo da man daga ƙasashen waje.
Sun zargi matatar da ƙoƙarin hana shigo da fetur, tare da kalubalantar ta da ta gabatar da hujjar cewa fetur ɗin da ake shigowa da shi Najeriya bai cika ƙa’idojin inganci ba.
Rahotanni sun ce matatar na nazarin takaita sayar da fetur ga manyan ‘yan kasuwa da ke ci gaba da shigo da man daga waje.
Matatar na zargin wasu ‘yan kasuwa da haɗa fetur ɗin da suka saya daga Dangote da na waje, lamarin da take ganin zai iya h
Rahoton ya ce Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillarsa ta kai dala biliyan 221 a faɗin nahiyar. Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke faɗi-tashin neman ingantaccen makamashi, lamarin da ke sake tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin jagorar fannin makamashi a Afirka. Rahoton wanda kamfanin binciken makamashi na Industrial Info Resources ya fitar, ya nuna cewa a halin yanzu ana bin diddigin manyan ayyukan samar da mai da iskar gas sama da 800 a ƙasashen Afirka daban-daban. Wannan rahoto ya nuna yadda manyan kamfanonin ƙ
Gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa kusan ‘yan kasuwa 40 da gobara ta shafa a yankin Small-Scale Industrial Area da ke Dakata, da jimillar kuɗi har Naira miliyan 100. An miƙa kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa ne a madadin Gwamnan Jihar Kano, yayin da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna matuƙar damuwa kan mummunar gobarar da ta haddasa asarar dukiya da kuma kawo cikas ga harkokin kasuwancin waɗanda abin ya shafa. Alhaji Umar Farouk ya ce tallafin ya kasance cikar alƙawarin da Gwamnan ya ɗauka na taimaka wa ‘yan kasuwar
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Najeriya, JAMB , ta bullo da sabon tsarin da zai bai wa ɗalibai damar tantancewa da kuma loda sakamakon jarabawarsu ta O’Level daga gidajensu, inda aka fara da sakamakon da Hukumar WAEC ke fitarwa. A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya fitar, sabon tsarin zai samar wa ɗalibai wata hanya mafi sauƙi ta kammala aikin, musamman a lokutan da ake samun cunkoso da matsalolin sadarwar intanet a cibiyoyin CBT . Hukumar ta ce ƙaddamar da tsarin na daga cikin ƙoƙarinta na sauƙaƙa ayyukanta, da sa su zama cikin sauri, aminci da
Kamfanin NNPC Limited da abokan hulɗarsa na OML 118 sun rattaba hannu kan muhimman yarjejeniyoyi da za su ciyar da aikin Bonga Southwest/Aparo gaba zuwa matakin yanke shawarar zuba jari na ƙarshe. A cewar wata sanarwa da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, Andy Odeh, ya fitar, ana sa ran aikin zai jawo zuba jari har dala biliyan 21 , abin da zai mayar da shi cikin manyan ayyukan hako mai daga teku da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. Ana sa ran aikin zai iya samar da gangar mai har 175,000 a kowace rana a lokacin da ya kai kololuwar samarwa. Babban Daraktan Gudanarwa na NNPC Limited, Bashir Ojula
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da masu zuba jari domin tabbatar da nasarar noman shinkafa a babbar gonar Jangwa-Agwatashi da ke ƙaramar hukumar Obi. Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa noman shinkafa, ƙara samar da abinci da kuma tabbatar da wadatar abinci a jihar. Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ziyarci gonar tare da wakilan kamfanonin da ke da hannu a aikin, inda ya sanar da faɗaɗa haɗin gwiwar domin kauce wa tsaiko da tabbatar da dorewar noma a gonar. A ƙarƙashin sabon tsarin, wani daga cikin kamfanonin zai kula da sarrafa da niƙa shinka
Bankin Standard Chartered Nigeria Limited ya haɗa gwiwa da Junior Achievement Nigeria (JAN) domin faɗaɗa damar matasan Najeriya samun horon ƙwarewar fasahar zamani, ta hanyar wani shiri na musamman mai suna Digital Bootcamp Program . Shirin na da nufin shirya matasa domin su samu ƙwarewar da ake buƙata a kasuwar aikin zamani da tattalin arzikin da ke ƙara dogaro da fasahar dijital. A cewar sanarwar, za a horas da matasa sama da 600 a jihohin Ondo, Abuja, Rivers da Kaduna. Za a gudanar da horon na tsawon kwanaki 10 , inda mahalarta za su samu horo na aikace-aikace kan fannoni daban-daban da suk
Wata babbar kasuwa mai suna SUFAYE Investment da ke Kano ta miƙa kayayyakin abinci da sauran kayayyakin da suka lalace ko suka ƙare wa’adin amfani da su, waɗanda darajarsu ta haura Naira miliyan 28 , ga Majalisar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano domin lalata su. Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Majalisar, Jamilu Mustapha, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano. Sakataren Zartarwa na Majalisar, Dr Ibrahim Garba-Muhammad, ya bayyana matakin da kamfanin ya ɗauka a matsayin abin a yaba, yana mai kira ga sauran kamfanoni da ’yan kasuwa a jihar da su yi koyi da
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN), Shehu Bello , ya ce matsalar da harkar noma a Najeriya ke fuskanta ba wai ƙarancin kuɗaɗen tallafi ba ce, sai dai ƙalubalen gano waɗanda suka cancanci tallafin, samun damar karɓar kuɗin da kuma dawo da lamunin noma. Bello ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin “Good Morning Nigeria” na gidan talabijin na ƙasa, NTA, kan batun “Cike Gibin Tallafin Noma a Najeriya.” Ya ce akwai hanyoyi da dama na samar da kuɗaɗe ga harkar noma, amma babban ƙalubalen shi ne yadda za a tabbatar da cewa kuɗin sun isa hannun manoman da suka dace,
Shugaban Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Kano ( KanInvest ), Dr. Muhammad Nazir Halliru, ya karɓi tawagar tsoffin shugabannin jam’iyyar PDP daga mazabu 11 na Ƙaramar Hukumar Nassarawa, waɗanda suka fice daga PDP suka koma jam’iyyar APC. Tawagar ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf , tana mai cewa matakin komawarsu APC ya samo asali ne daga irin nasarori da ayyukan raya jihar da gwamnatin ke aiwatarwa. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Shugaban tsoffin shugabannin PDP da suka koma APC, Alhaji Sani Suleiman Dakata , ya ce sun yanke shawarar mara wa gwamnatin jihar baya ne
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC , ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric , sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa. NERC ta ce matakin ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Agustan 2026 , bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta 2023 . Hukumar ta bayyana cewa Kaduna Electric ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, wanda ya sa jimillar bashin kamfanin ya kai kusan naira biliyan 456.5 . NERC ta ce a shekarar 2025, kamfanin ya biya kash
Ƙungiyar Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX Group) ta bayyana cewa darajar kasuwar kamfanonin da aka jera a kasuwar hannayen jari ta ƙaru daga kusan Naira tiriliyan 30 a watan Mayun 2023 zuwa sama da Naira tiriliyan 150 a halin yanzu. Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NGX Group, Temi Popoola , ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shi da shugaban NGX da Darakta Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) suka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Popoola ya ce tawagar ta yi wa Shugaban Ƙasa bayani kan yadda kasuwar hannayen jari ke bu
Shirin na gudana ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Kaduna Markets Development and Management Company (KMDMC) da Kaduna Geographic Information Service (KADGIS) , domin bai wa masu shaguna da sauran kadarorin kasuwanci da suka cancanta damar samun Takardar Shaidar Mallaka (Certificate of Occupancy – C of O) ga kowane shago ko rukunin kasuwanci da suka mallaka. Sabon tsarin ya shafi shaguna da ke cikin kasuwanni, manyan cibiyoyin kasuwanci (shopping malls), plazas da sauran gine-ginen kasuwanci masu ɗauke da raka’o’i da dama. Ana sa ran tsarin zai tabbatar da ingantacciyar mallaka ta doka, kare h