Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.

Shettima ya bayyana hakan ne a New York yayin wata ganawa da ’yan Najeriya mazauna Amurka, a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

A cewar wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, Shettima ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako.

Ya ce ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 55, yayin da kasuwar musayar kuɗaɗen waje ke samun sauƙi, sannan tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kashi 4.45 cikin 100 a rubu’i na biyu na bana.

Mataimakin shugaban ya ce gwamnatin na mayar da hankali kan inganta ilimi, lafiya, kimiyya da fasaha da noma, tare da samar da yanayin da zai ƙarfafa zuba jari.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su taka rawa wajen ci gaban ƙasar, ta hanyar amfani da ilimi, ƙwarewa da basirar da suke da su.