NDLEA ta yi wa mutum 53,843 maganin shan miyagun ƙwayoyi cikin shekaru biyar
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta yi wa mutane 53,843 da ke fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi magani cikin shekaru biyar, a cibiyoyinta da ke jihohi 31 na ƙasar. Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani gangami na wayar da kan al’umma da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya. Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana shirin hukumar na kawar da shan miyagun ƙwayoyi da kuma yaƙi da safarar su a faɗin ƙasar. Marwa ya ce matsalar shan miyagun ƙwayoyi na ƙara ta’azzara, inda masu amfani da su ke fuskantar barazan
