Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta yi wa mutane 53,843 da ke fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi magani cikin shekaru biyar, a cibiyoyinta da ke jihohi 31 na ƙasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani gangami na wayar da kan al’umma da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana shirin hukumar na kawar da shan miyagun ƙwayoyi da kuma yaƙi da safarar su a faɗin ƙasar.

Marwa ya ce matsalar shan miyagun ƙwayoyi na ƙara ta’azzara, inda masu amfani da su ke fuskantar barazana ga lafiyar jikinsu da ƙwaƙwalwarsu, musamman matasa.

Ya ƙara da cewa hukumar na ci gaba da ƙoƙarin wayar da kan jama’a game da illolin shan miyagun ƙwayoyi, tare da samar da hanyoyin taimaka wa waɗanda suka kamu da matsalar domin su samu sauƙi.

NDLEA na kuma ci gaba da gudanar da samamen kama miyagun ƙwayoyi, ciki har da hodar iblis da tabar wiwi da sauran nau’o’in kayan maye, a filayen jiragen sama, tashoshin mota da sauran wuraren da ake zargin ana safarar su.

Hukumar ta ce ƙoƙarin yaƙi da matsalar ya haɗa da wayar da kai, jiyya da kuma dakile fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin Najeriya.