top stories
Dangote zai ƙaddamar da aikin gina matatar mai a Kenya
Attajirin Afirka, Aliko Dangote, zai aza harsashin gina wata sabuwar matatar man fetur a gabar tekun Kenya a yau. Matatar za a gina ta ne a yankin Lamu, kuma Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce aikin zai taimaka wajen rage tasirin sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya ga ƙasar. Sai dai aikin ya fuskanci ce-ce-ku-ce, inda aka samu arangama tsakanin ’yan sanda da wasu masu zanga-zanga da ke ikirarin cewa filin da ake shirin gina matatar mallakinsu ne. Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan illar da suka ce aikin zai iya haifarwa ga muhalli. Duk da waɗannan ƙorafe-ƙorafe da kuma
azubairu (legacy byline) · 30 Sat, 2026, 12:38
Attajirin Afirka, Aliko Dangote, zai aza harsashin gina wata sabuwar matatar man fetur a gabar tekun Kenya a yau.
Matatar za a gina ta ne a yankin Lamu, kuma Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce aikin zai taimaka wajen rage tasirin sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya ga ƙasar.
Sai dai aikin ya fuskanci ce-ce-ku-ce, inda aka samu arangama tsakanin ’yan sanda da wasu masu zanga-zanga da ke ikirarin cewa filin da ake shirin gina matatar mallakinsu ne.
Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan illar da suka ce aikin zai iya haifarwa ga muhalli.
Duk da waɗannan ƙorafe-ƙorafe da kuma umarnin wata kotu na dakatar da aikin, Dangote na ci gaba da shirin fara gina matatar.