Har yanzu ana ci gaba da muhawara kan makomar takarar Farfesa Ali Isa Pantami na neman zama gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke tikitin tsohon Ministan Sadarwa, wanda jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar.

Usman Aliyu Garry ne ya shigar da ƙarar, inda ya ƙalubalanci tsarin da jam’iyyar PDP ta bi wajen tsayar da Pantami a matsayin ɗan takararta.

Kotun ta ce tsarin da PDP ta bi bai dace da ƙa’idojin jam’iyyar da kuma dokokin zaɓe ba, saboda ya sa aka cire wasu daga cikin waɗanda aka tantance domin shiga zaɓen fidda gwani.

Mai shari’a Amina Mohammed ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Gombe.

Pantami dai ya koma PDP ne bayan ya fice daga APC, wadda ya yi wa takarar gwamnan Gombe a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Sai dai hukuncin kotun ya buɗe sabon babi kan makomar takarar Pantami da kuma wanda zai wakilci PDP a zaɓen gwamnan Gombe na 2027.