Wata Babbar Kotun Jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum mai shekara 50, Abubakar Biniya, hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekara 10 bayan samun sa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 11 fyaɗe.

Alƙali Muhammad El Usman ne ya jagoranci zaman kotun da ta samu Biniya da laifi.

A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa, Abbas Rufa’i Wangara, ya fitar, Biniya ya aikata laifin ne a watan Janairun 2024 a unguwar Galadanchi da ke Ringim.

Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu shida da kuma hujjoji biyar, ciki har da rahoton likita, domin tabbatar da zargin.

Biniya ya ba da shaida a lokacin da yake kare kansa, amma bai gabatar da wata shaida ba.

A hukuncin da ya yanke, alƙalin ya ce kotun ta yi la’akari da roƙon sassauci da wanda ake tuhuma ya yi, da kuma kasancewar wannan ne karon farko da aka same shi da aikata laifi.

Baya ga ɗaurin shekara 10, kotun ta kuma umarci Biniya ya biya yarinyar diyya ta Naira 500,000.

Kotun ta bayar da umarnin saka sunan Biniya cikin rajistar masu aikata laifukan cin zarafi ta hanyar lalata ta Jihar Jigawa.

Haka kuma, ta umarci a yaɗa labarin hukuncin ta gidajen rediyo bisa tanadin dokar hana cin zarafin mutane ta jihar.

Kotun ta bai wa ɓangarorin da abin ya shafa wa’adin watanni uku domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin.