Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta cimma yarjejeniyar sake fara aikin haƙar uranium a yankin Madaouela, matakin da ake sa ran zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, kamfanin da zai gudanar da aikin zai biya dala miliyan 10 a matsayin kuɗin farko, tare da samar da kusan guraben ayyukan yi 1,000.

Kamfanin dillancin labaran Nijar, ANP, ne ya ruwaito hakan.

Madaouela na daga cikin manyan wuraren da ke da arzikin uranium a Nijar, inda ake kiyasta cewa yankin na ɗauke da tan dubu 52 da ɗari 800 na ma’adinin.

An farfaɗo da aikin ne bayan da mahukuntan Nijar suka kawo ƙarshen yarjejeniyar da suka yi da kamfanin GoviEx na ƙasar Canada.

Matakin na daga cikin manufofin gwamnatin mulkin sojan Nijar na ƙara ikon gwamnati kan albarkatun ma’adinan ƙasar da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga.