Wasu ’yan Najeriya 105 sun dawo gida daga Afirka ta Kudu, yayin da ake ci gaba da fargabar yiwuwar hare-hare kan ’yan ƙasashen waje gabanin wa’adin 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka sanya.
’Yan Najeriyar sun isa Lagos da misalin ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, a cikin jirgin South African Airways, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana.
Ma’aikatar ta ce tun daga watan Yuni, gwamnati ta taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya 1,821 daga Afirka ta Kudu, sakamakon sake ɓarkewar hare-hare kan baƙi da ’yan Afirka.
Kakakin ma’aikatar, Femi Adeniyi, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin dawo da wasu ’yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali saboda fargabar tsaro.
Dawowar tasu na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin 30 ga Satumba, ranar da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka sanya wa ’yan ƙasashen waje da ba su da takardun zama wa’adin barin ƙasar.
A baya, an sanya irin wannan wa’adi a ranar 30 ga Yuni, lamarin da ya janyo zanga-zangar adawa da baƙin haure a wasu sassan Afirka ta Kudu, inda aka samu rahotannin tashin hankali da sace-sace.
Hukumomin Afirka ta Kudu sun jaddada cewa gwamnati ce kaɗai ke da alhakin aiwatar da dokokin shige da fice, tare da yin gargaɗin kada mutane su ɗauki doka a hannunsu ko kai hari kan ’yan ƙasashen waje.
Najeriya ba ita kaɗai ce ke taimaka wa ’yan ƙasarta barin Afirka ta Kudu ba, yayin da Malawi, Zimbabwe, Uganda, Ghana da Mozambique su ma suka dawo da wasu daga cikin ’yan ƙasarsu.
