Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta tarwatsa wani ɓoyayyen dakin sarrafa ƙwayar methamphetamine a jihar Enugu.
Hukumar ta ce ana zargin dakin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ’yan Najeriya da Mexico.
An kama ’yan Najeriya biyu, Chukwu Obumneme Christopher, mai shekaru 45, da Chukwu Georginus Monday, mai shekaru 60, waɗanda aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Enugu.
Ana tuhumar mutanen da laifuka biyar, ciki har da haɗa baki, ɗaukar nauyin ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar sinadarai da ake amfani da su wajen ƙera methamphetamine.
NDLEA ta ce mutanen biyu sun amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu, kuma za a fara sauraron shari’ar a ranar 21 ga Oktoba.
Hukumar ta ƙara da cewa wasu mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wani ɗan Mexico, sun tsere.
Binciken NDLEA ya nuna cewa an bibiyi zirga-zirgar Christopher tsakanin Lagos, Enugu da Anambra tun watan Disamban 2025, kafin a gano dakin sarrafa ƙwayoyin a wani gida da ke Obeagu, Enugu.
An kuma ƙwace sinadarai da kayan aikin da hukumar ta ce za su iya samar da methamphetamine mai yawa domin kasuwanci.
Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ce samamen ya ƙara tabbatar da cewa Najeriya ba za ta bari ta zama mafaka ga ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa ba.
