Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya naɗa Kashim Ibrahim-Imam a matsayin shugaban kwamitin, yayin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, zai zama mataimakinsa.
Sanarwar naɗin ta fito ne ranar Alhamis daga Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku, wanda kuma babban mataimaki ne ga Atiku kan harkokin yaɗa labarai.
An kuma naɗa Sanata Austin Akobundu a matsayin Darakta-Janar kuma Manajan Yaƙin Neman Zaɓen, inda zai jagoranci gudanar da ayyukan kwamitin da aiwatar da dabarunsa.
Kwamitin ya ƙunshi daraktoci mataimaka shida da daraktoci 30 da aka ba su nauyin kula da fannoni daban-daban. Dele Momodu zai jagoranci sashen yaɗa labarai da sadarwa, yayin da Dino Melaye zai jagoranci harkokin tuntuɓa da wayar da kan jama’a.
Haka kuma, Mohammed Hayatu-Deen zai jagoranci ƙungiyar tsara manufofi, tare da Farfesa Mohammed Sagagi da wasu mambobi.
A cewar sanarwar, an tsara kwamitin ne domin mayar da hankali kan matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da tsadar abinci da sufuri, rashin aikin yi, matsalar tsaro da raguwar ƙarfin sayen jama’a.
Naɗin El-Rufai ya zo ne a daidai lokacin da yake fuskantar binciken hukumomin Najeriya kan zarge-zargen da ake yi masa, waɗanda ya musanta.
Kwamitin zai jagoranci ayyukan yaƙin neman zaɓen Atiku da sauran harkokin shirye-shiryen jam’iyyar ADC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
