Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce binciken da ake yi kan lamarin da ya faru a wani sansanin sojin sama na Birtaniya da dakarun Amurka ke amfani da shi, ya nuna alamun yiwuwar hannu daga wasu ƙasashen waje.

An kama wasu maza biyar bisa zargin shirya aikata ta’addanci a sansanin, lamarin da ya jawo bincike daga hukumomin Birtaniya.

Da yake magana da gidan talabijin na Fox News, Rubio ya ce ana sa ran samun ƙarin bayanai game da lamarin a cikin kwanaki masu zuwa.

Sai dai tun da farko, Sakataren Tsaron Birtaniya ya ce bai kamata a yi gaggawar tabbatar da cewa wasu ‘yan ƙasashen waje na da hannu a lamarin ba.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kuma soki matakin ‘yan sandan yaƙi da ta’addanci na Birtaniya na bayar da belin mutanen biyar.

Sansanin sojin da abin ya shafa na daga cikin wuraren da Amurka ta yi amfani da su wajen kai hare-hare kan Iran. Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zargin cewa tana da hannu a lamarin da ake bincike a kansa.