Firaministan Faransa, Sébastien Lecornu, ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na ƙara tsananta zanga-zangar ɗaliban makarantun sakandare a faɗin ƙasar ba zai haifar da wani amfani ba.
Fiye da mutum 160 ne aka kama a ranar Litinin sakamakon zanga-zangar.
A wani saƙo da ya wallafa a kafar sada zumunta, Mista Lecornu ya yi nuni da rahotannin amfani da tartsatsin wuta da kuma tashe-tashen hankula yayin zanga-zangar.
Zanga-zangar ta fara ne a birnin Paris a makon da ya gabata, inda ɗalibai suka rufe wasu makarantu na tsawon kwanaki domin nuna rashin amincewarsu da yanayin da suke karatu a ciki.
Dalilan zanga-zangar sun haɗa da cunkoson ɗalibai a ajujuwa, yawan ayyukan makaranta da kuma ƙarancin malamai.
Tun daga lokacin ne zanga-zangar ta yaɗu zuwa wasu sassan ƙasar.
