Gwamnatin Ghana ta dakatar da aiwatar da dokar da ta haramta wa’azi da talla a cikin motocin haya da na jama’a yayin da suke tafiya.

Sabuwar dokar zirga-zirgar ta tanadi hukuncin ɗaurin watanni takwas a gidan yari ko tara da ta haura dala 52 ga duk wanda ya karya dokar.

Rahoton BBC da aka fitar kan dokar ya janyo muhawara a Ghana, musamman dangane da tasirinta ga ’yancin addini da bayyana ra’ayi.

Mai magana da yawun gwamnatin Ghana, Felix Kwakye Ofosu, ya shaida wa BBC a ranar Juma’a cewa akwai buƙatar sake nazarin dokar, bayan da wasu shugabannin addinai suka nuna damuwa kan yadda za a aiwatar da ita.

Ya ce gwamnati ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shugabannin addinai da masu ibada, don haka ta dakatar da aiwatar da dokar na ɗan lokaci domin gudanar da ƙarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da neman fahimtarsu kafin a fara aiwatar da ita.

Ghana ƙasa ce da Kiristoci suka fi yawa, kuma yin wa’azi a cikin motocin haya, musamman bas-bas, ya zama ruwan dare a sassan ƙasar.

Sai dai dokar ta haramta wannan aiki ne domin kauce wa abubuwan da za su iya tayar da hankalin fasinjoji ko kawo cikas yayin tafiya, ba tare da la’akari da addinin wanda ke yin wa’azin ba.

Ra’ayoyin al’ummar Ghana sun kasu kashi biyu kan batun. Masu adawa da wa’azi a cikin motocin haya na ganin cewa hakan na iya damun fasinjoji, tare da jefa lafiyarsu cikin haɗari idan ya ɗauke hankalin direba.

A gefe guda kuma, masu goyon bayan wa’azin na ganin cewa yin bishara muhimmin ɓangare ne na addinin Kirista, kuma kundin tsarin mulkin Ghana ya tanadi ’yancin addini da bayyana imanin mutum.

Dakatar da aiwatar da dokar na ɗan lokaci na nufin cewa ana buƙatar ƙarin tattaunawa kan yadda za a daidaita ’yancin gudanar da ibada da kuma haƙƙin fasinjoji na samun kwanciyar hankali da tsaro yayin tafiya.