Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da fara rarraba ruwan sha daga ma’ajiyar Goron Dutse Reservoir zuwa sassan birnin Kano, bayan shafe sama da shekaru 30 ba ta aiki.
Gwamnan ya bayyana farfaɗo da ma’ajiyar a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen inganta samar da ruwan sha ga al’ummar Kano.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ma’ajiyar na da damar adana kusan lita miliyan 39.8 na ruwa.
Ya ce ana tura ruwan daga matatar Challawa zuwa Goron Dutse, daga inda ake rarraba shi ga al’ummomin sassa daban-daban na birnin Kano.
A cewarsa, kamfanin CCECC ne ya aiwatar da aikin da ya lakume kusan Naira biliyan 11 , wanda ya haɗa da aikin matatar Challawa da kuma shimfiɗa bututun da ke kai ruwa Goron Dutse mai tsawon kusan kilomita 15.6 .
Kwamishinan ya ƙara da cewa, duk da cewa an tsara kammala aikin a watan Disamba na 2026, an fara rarraba ruwan tun kafin wa’adin da aka tsara.
