Sojin Saman Najeriya na neman na’urorin bayanan jirgin da ya yi hatsari a Ondo
Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta fara ƙoƙarin gano na’urorin da ke ɗauke da bayanan muryoyin matuƙan jirgi da kuma bayanan jirgin da ya yi hatsari a yankin Igbokoda, da ke Ƙaramar Hukumar Ilaje a Jihar Ondo. Babban jami’in kula da ƙa’idoji da tantancewa na rundunar, Air Vice Marshal Ebimobo Ebiowe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wurin da hatsarin ya faru a ranar Juma’a. Jirgin mai saukar ungulu, wanda ke gudanar da aikin yau da kullum daga Benin, babban birnin Jihar Edo, zuwa Legas, ya faɗo cikin wata fadama kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda a ranar
