Hukumar Kula da Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce mutum 263 sun mutu sakamakon zazzabin Lassa, yayin da aka tabbatar da mutum 1,115 sun kamu da cutar tsakanin watan Janairu zuwa ranar 20 ga Satumba, 2026.

Hukumar ta bayyana cewa adadin mace-macen ya kai kashi 23.6 cikin 100, wanda ya haura na makamancin lokacin a shekarar 2025, lokacin da ya kai kashi 18.5 cikin 100.

Jihohin Ondo, Bauchi, Taraba, Edo da Benue ne suka fi yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda suka haɗa kusan kashi 87 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu a ƙasar.

NCDC ta danganta yawaitar mace-macen da jinkirin kai marasa lafiya asibiti domin samun kulawar likitoci, da kuma wasu ƙalubale da suka haɗa da tsadar jinya, rashin tsaftar muhalli da ƙarancin wayar da kan al’umma a wasu yankuna.

Hukumar ta buƙaci jama’a da ma’aikatan lafiya su ƙara himma wajen ɗaukar matakan kariya da kuma gano masu cutar cikin gaggawa domin rage mace-mace da yaɗuwarta.

Zazzabin Lassa cuta ce da ake iya ɗauka daga berayen da suka gurɓata abinci ko muhallin zama, sannan tana iya yaɗuwa tsakanin mutane ta hanyar mu’amala da jinin ko ruwan jikin wanda ya kamu da ita.

NCDC ta jaddada muhimmancin tsaftace muhalli, adana abinci a cikin kwantena masu murfi da kuma gaggauta zuwa asibiti idan mutum ya fara nuna alamun cutar.