Jam’iyyar hamayya ta ADC a Najeriya ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, a wani mataki na shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.

Yayin ƙaddamar da kwamitin a Abuja, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin masu kishin ƙasa da kuma gogaggun mutane a harkokin siyasa da tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Sanata Augustine Okwudiri Akobundu ne zai jagoranci kwamitin, tare da taimakon wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

El-Rufai dai na fuskantar bincike kan zarge-zargen aikata laifuka, kuma rahotanni sun nuna cewa yana hannun hukumomin ƙasar.

Atiku Abubakar ya ce kwamitin na da babban nauyi na taimaka wa ADC wajen isar da saƙonta ga ’yan Najeriya, tare da bayyana manufofi da hanyoyin da jam’iyyar ke ganin za ta bi wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Ya ƙara da cewa waɗanda aka naɗa za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara da gudanar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

ADC na daga cikin jam’iyyun siyasa da ke shirin fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen a faɗin Najeriya.