Ƙungiyar ƙwadago ta TUC reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta umarci mambobinta da su ci gaba da zuwa wuraren aikinsu, tana mai bayyana cewa ba ta goyi bayan yajin aikin sai baba-ta-gani da babbar ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ayyana ba.
TUC ta bayyana cewa ba ta halarci taron da aka yanke shawarar fara yajin aikin ba, don haka ba ta amince da matakin da aka ɗauka ba.
Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci dukkan mambobinta da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Haka kuma, TUC ta gargaɗi mambobinta da kada su bari a tilasta musu shiga yajin aikin, tana mai jaddada buƙatar warware rikicin da ya shafi malamai ta hanyar tattaunawa.
Ƙungiyar ta ce yin sulhu ta hanyar tattaunawa zai taimaka wajen kauce wa kawo cikas ga harkokin ilimi da kuma hana ɗalibai rasa lokacin karatu.
