Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta fara ƙoƙarin gano na’urorin da ke ɗauke da bayanan muryoyin matuƙan jirgi da kuma bayanan jirgin da ya yi hatsari a yankin Igbokoda, da ke Ƙaramar Hukumar Ilaje a Jihar Ondo.

Babban jami’in kula da ƙa’idoji da tantancewa na rundunar, Air Vice Marshal Ebimobo Ebiowe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wurin da hatsarin ya faru a ranar Juma’a.

Jirgin mai saukar ungulu, wanda ke gudanar da aikin yau da kullum daga Benin, babban birnin Jihar Edo, zuwa Legas, ya faɗo cikin wata fadama kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda a ranar Litinin.

Hatsarin ya yi sanadin mutuwar dukkan mutane 25 da ke cikin jirgin, a cewar rahoton.

Jami’ai sun bayyana cewa jirgin ya faɗo ne tare da rabuwa gida biyu, inda babban sashensa ya nutse gaba ɗaya cikin fadamar.

Sun ƙara da cewa jirgin ya nutse zuwa zurfin kusan mita 30 a cikin ruwan fadamar, lamarin da ke ƙara wahalar aikin ceto da kuma gano muhimman na’urorin da za su taimaka wajen gano musabbabin hatsarin.

Ana sa ran bayanan da za a samu daga na’urorin za su taimaka wa masu bincike wajen fahimtar abin da ya faru kafin jirgin ya faɗo da kuma gano musabbabin aukuwar hatsarin.