Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta yi kakkausar suka kan harin da wasu Yahudawa ’yan kama wuri zauna suka kai wa jami’an diflomasiyyar Turai da wani magajin gari na Faransa a Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sayen ƙarin taragon jiragen ƙasa da na’urorin tsaro na zamani domin inganta sufurin jiragen ƙasa da yaƙi da laifuka, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane da lalata layin dogo.
Hukumar agaji ta ƙasa da ƙasa, ICRC, ta ce matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta ƙaru a wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya, inda adadin mutanen da ke fama da ita ya tashi daga kusan 17,000 zuwa 20,000, bisa bayanan da aka tattara daga cibiyoyin lafiya.
Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa a jihohi 12 na Nijeriya gabanin zaɓen 2027, yayin da shugabannin jam’iyyar APC za su wakilce shi a sauran jihohin ƙasar.
Najeriya ta ci gaba da gudanar da shari’o’in masu zargin aikata laifukan ta’addanci, inda a ranar 16 ga Oktoba aka yanke wa mutum 21 hukuncin ɗauri kan laifuka daban-daban da suka shafi ta’addanci, ciki har da wani ɗan ƙasar China, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya kusanci dala 110 kan kowace ganga, a karon farko tun daga watan Mayun 2026, sakamakon fargabar ƙarin tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
An zaɓi Najeriya a matsayin mamba a Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) na wa’adin shekarun 2027 zuwa 2029, bayan ta samu ƙuri’u 172 cikin ƙuri’u 181 da aka kaɗa a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.
Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a ƙara zuba jari wajen tallafa wa matan da ke zaune a karkara, domin bunƙasa noma, inganta samar da abinci da kuma ƙarfafa tattalin arziki.
Mahukuntan Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Koyon Shari’a ta Aminu Kano (AKCILS) sun musanta jita-jitar da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta cewa makarantar na hana ɗalibai mata masu sanya niƙabi shiga harabar kwalejin.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama mutane 1,860 tare da ƙwace kilogiram 5,409.814 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano tsakanin Janairu da Satumba 2026.
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun bayyana cewa ƙasar ta samu sabbin manyan makamai bayan yaƙin da ta yi da Amurka da Isra’ila, tare da gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari.
Shugabannin ƙasashen duniya sun ci gaba da aika saƙonnin fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga Paparoma Leo, bayan an yi masa tiyatar da aka ce an cire wani ɓangare na huhunsa na dama a birnin Rome.
Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe ƙofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke Abuja a ranar Talata, domin neman a sauya tsarin lissafa kuɗaɗen fanshonsu da kuma biyan buƙatunsu.
GARGADI GAME DA ABUBUWAN DA KE CIKI: Wannan rahoton ya na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali da suka shafi kashe kai."Na bayar da kyautar 50,000 ...
Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu ’yan Najeriya biyu da aka yi a Afirka ta Kudu, tare da neman gudanar da bincike cikin gaggawa kan musabbabin mutuwarsu. Mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya ce lamarin ya ƙara jefa shakku kan tsaron baƙi a Afirka ta Kudu, musamman ’yan Afirka, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ƙyamar baƙi a ƙasar. Ya ce zargin hannu ko sakaci daga jami’an tsaro a mutuwar ‘yan Najeriya na ƙara dagula dangantakar da tuni ta yi tsami tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu. Gwamnatin Najeriya ta buƙaci hukumomin
Ga mazauna yankunan da ke kusa da Kogin Hadejia da sauran wuraren da ruwa ke taruwa a Jihar Jigawa, damina lokaci ne da ke haɗa fata da fargaba . Ruwan sama na kawo albarka, domin yana cika koguna da tafkuna, yana samar da ruwa ga dabbobi, yana taimaka wa manoma wajen noma, sannan ya zama hanyar samun abinci da kuɗin shiga ga dubban iyalai. Masunta na dogaro da koguna da tafkuna wajen gudanar da sana’arsu, yayin da masu kiwo ke samun ruwa da ciyawar da dabbobinsu ke buƙata. Sai dai a gefe guda, damina na zuwa da wata babbar fargaba — ambaliya . Wannan fargabar ta sake kunno kai bayan hukumomin
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwato kwayoyi daban-daban 5,916 da tubalan tabar wiwi guda biyar . Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam , ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Tijjani Murtala . A cewar sanarwar, an gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri a yankunan rundunonin ’yan sanda na Kazaure, Gumel, Miga, Dutse, Sundumina, Taura, Babura, Ringim, Sara da Aujara . Rundunar ta ce daga cikin abubuwan da jami’
Gwamnatin Jigawa ta amince da ware Naira biliyan 12.68 domin gina sababbin gine-gine, samar da kayan aiki da gyara wasu makarantun sakandare sama da 50 a faɗin jihar. A cewar gwamnatin jihar, aikin zai shafi makarantun sakandare da ke sassa daban-daban na Jigawa, kuma an tsara shi ne domin magance ƙarancin kayayyakin more rayuwa a makarantu tare da inganta yanayin karatu ga ɗalibai da aikin koyarwa ga malamai. Ayyukan sun haɗa da gina sababbin gine-ginen makarantu, samar da kayan aiki da gyaran wasu gine-ginen da ake da su. Gwamnatin ta ce zuba jarin zai taimaka wajen rage cunkoso da matsin la