Hukumar ta kuma bayyana cewa kotuna sun samu mutane 89 da laifi, yayin da ta shigar da sabbin ƙara 126 a gaban kotu cikin watanni tara. A halin yanzu, ana ci gaba da sauraron wasu ƙara 135 a gaban Babbar Kotun Tarayya.
Rundunar NDLEA ta musamman a Kano ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Talata.
Rundunar NDLEA ta musamman a Kano ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Talata.
NDLEA Ta Taimaka Wa Mutane 1,700
Rundunar ta ce ta gudanar da shirye-shiryen ba da shawarwari, magani da gyaran hali ga kusan mutane 1,700 da matsalar shan miyagun ƙwayoyi ta shafa.
Haka kuma, hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kusan 420 a makarantu da al’ummomi domin faɗakar da mutane kan illolin shan miyagun ƙwayoyi da kuma hanyoyin yaƙi da fataucinsu.
NDLEA Ta Yi Kira Ga Al’umma
Kwamandan rundunar NDLEA a Kano, CN DY Lawal, ya yaba wa Mohamed Buba Marwa bisa jagorancinsa da ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan hukumar.
Lawal ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su riƙa kai wa hukumar sahihan bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da suka shafi fatauci da amfani da su.
Ya jaddada cewa haɗin kan jama’a da jami’an tsaro na da muhimmanci wajen rage safarar miyagun ƙwayoyi da inganta tsaron al’umma a faɗin Jihar Kano.
