Yayin da duniya ke bikin Ranar Abinci ta Duniya a ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, sabbin alkaluman hukumar ICRC sun nuna yadda matsalar ƙarancin abinci ke ƙara ta’azzara a wasu sassan Najeriya.
Bayanan hukumar sun nuna cewa matsalar ta ƙaru sosai a jihohin arewa maso gabashin ƙasar, inda rikice-rikicen tsaro da ƙarancin abinci ke ƙara jefa al’ummomi cikin mawuyacin hali.
ICRC ta ce bayanan da aka tattara daga asibitoci huɗu da cibiyoyin lafiya shida sun nuna cewa adadin mutanen da ke fama da matsalar ya tashi daga kusan 17,000 a bara zuwa 20,000 cikin ƙasa da shekara guda.
Hukumar ta tattara alkaluman ne daga watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2026.
Mata da yara na cikin waɗanda matsalar ta fi shafa
A cewar ICRC, ƙananan yara, mata masu juna biyu da kuma mata masu shayarwa na daga cikin waɗanda suka fi fuskantar barazanar ƙarancin abinci mai gina jiki.
Hukumar ta danganta matsalar da ƙarancin abinci da ake fuskanta a yankin, wanda ya ƙara tsananta halin da iyalai da dama ke ciki.
ICRC ta kuma bayyana cewa matsalar ta ƙaru a Mubi, da ke jihar Adamawa, inda adadin mutanen da abin ya shafa ya kai 5,700, daga 4,600 watanni tara da suka gabata.
Matsalar tsaro na shafar noman abinci
Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga samar da abinci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Saminu Samiyu, wani manomi a yankin, ya ce barazanar abubuwan fashewa a gonaki ta tilasta masa rage girman gonar da yake nomawa, lamarin da ya shafi yawan abincin da yake iya samarwa.
Matsalar ba ta shafi Saminu kaɗai ba, domin wasu manoma da dama sun rage ko kuma sun daina noma saboda barazanar tsaro.
Hakan na ƙara rage yawan amfanin gona da ake samu, tare da ƙara matsin lamba kan wadatar abinci da rayuwar al’ummomin yankin.
Ana hasashen miliyoyin ’yan Najeriya za su fuskanci ƙarancin abinci
Rahotanni sun kuma nuna cewa akwai hasashen cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 34 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a shekarar 2026.
