Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Muhammad Goje, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an samar da kayayyakin ne domin inganta yanayin aikin jami’an da kuma ƙara musu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da rigunan ruwa guda 900, takalman roba guda 900, barguna guda 900, fitilun hannu guda 900 da gidajen sauro guda 900, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko, Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara Kan Harkokin Tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, ya bayyana cewa Jihar Yobe ta samu masu tsaron dazuka 1,000 a rukunin farko ƙarƙashin wani shiri na Gwamnatin Tarayya.
Ya ce an zaɓo jami’an ne daga ƙananan hukumomi bakwai da matsalolin tsaro suka fi shafa, waɗanda suka haɗa da Gulani, Gujba, Damaturu, Tarmuwa, Bursari, Yunusari da Geidam.
A cewarsa, jami’ai 886 ne suka kammala horonsu a watan Disamban 2025, kafin daga bisani su sake samun ƙarin horo daga Rundunar Sojin Najeriya.
Raba babura da sauran kayayyakin aikin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa ayyukan masu tsaron dazuka, musamman a yankunan da ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
