remi tinubu

Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne a saƙonta na bikin Ranar Matan Karkara ta Duniya ta shekarar 2026, wadda ake gudanarwa a ranar 15 ga Oktoba. Ta yaba da jajircewa da muhimmiyar gudunmawar da mata a karkara ke bayarwa wajen ci gaban al'ummomi da ƙasashe.

Ta ce bikin na bana yana da muhimmanci na musamman, kasancewar ya zo ne a cikin Shekarar Manoma Mata ta Duniya, wanda ke ƙara jaddada rawar da mata ke takawa wajen tabbatar da dorewar samar da abinci da bunƙasar tattalin arzikin karkara.

Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a faɗaɗa damar da mata a karkara ke da ita wajen mallakar ƙasa, samun rance, horo, fasahohin zamani da hanyoyin kasuwanci, domin inganta ayyukansu da yanayin rayuwarsu.

A cewarta, tallafa wa mata a karkara zai amfani iyalai, ya taimaka wajen bunƙasa al'ummomi, tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ta jaddada muhimmancin samar wa mata damar da za su taimaka musu su taka rawar gani wajen noma da samar da abinci, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya.