Tsofaffin sojojin sun gudanar da zaman dirshan a ƙofar ofishin, yayin da sojoji masu ɗauke da makamai suka tare ƙofar shiga harabar hukumar, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan da wasu tsofaffin sojojin suka gudanar da makamanciyar zanga-zanga a Ma’aikatar Tsaro a watan Satumba, inda suka buƙaci ƙarin kuɗaɗen fansho sakamakon ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke bakin aiki.

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yi alƙawarin cewa za a biya tsofaffin sojojin ƙarin kuɗaɗen fansho a watan Oktoba.

Sai dai Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Sojojin Najeriya, Laftanar Kanal Innocent Azubike, ya zargi hukumar fanshon da amfani da tsarin lissafin kuɗaɗen fansho wanda, a cewarsa, bai dace da adadin kuɗin da ya kamata a riƙa biyansu ba.

Tsofaffin sojojin na neman a sake duba tsarin domin tabbatar da cewa ana biyan su fansho bisa ƙa'idojin da suka dace, musamman bayan ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke ci gaba da aiki.

Har yanzu, ana buƙatar ƙarin bayani daga hukumar fanshon kan matakan da take ɗauka domin warware matsalolin da tsofaffin sojojin suka gabatar.

Zanga-zangar tsofaffin sojojin Najeriya