Firaministan Australia, Anthony Albanese, da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, na daga cikin shugabannin da suka aika saƙonnin fatan alheri da addu’o’in samun sauƙi ga Fafaroman.

Haka kuma, Firaministan Canada, Mark Carney, ya bayyana fatansa na ganin Paparoman ya samu ƙarfi da kwarin gwiwa daga addu’o’in mutanen da ya taɓa taimakawa a rayuwarsa.

Tun da farko, fadar Vatican ta bayyana cewa an cire wani ɓangare na huhun dama na Paparoma Leo yayin tiyatar da aka gudanar a Rome.

A cewar rahoton BBC, ana jiran sakamakon wasu gwaje-gwajen da aka gudanar domin tantance halin da lafiyar Paparoman take ciki.

Rahoton ya ƙara da cewa an mayar da Fafaroman ɗakinsa na asibiti, inda ake sa ran zai fara murmurewa bayan tiyatar.

Ana ci gaba da sa ido kan halin lafiyarsa, yayin da saƙonnin addu’o’i da fatan samun sauƙi daga shugabannin duniya da sauran jama’a ke ci gaba da zuwa.