Lamarin ya faru ne ranar Asabar da ta gabata, lokacin da tawagar jami’an diflomasiyyar ke ziyartar yankin domin duba yadda manoman Falasɗinawa ke gudanar da girbin zaitun.
Rahotanni sun ce wasu mazauna matsugunan Isra’ila da suka rufe fuskokinsu sun farfasa gilashin motar da ke ɗauke da jami’an diflomasiyyar Belgium, sannan suka kai hari ga magajin garin Aulnoye-Aymeries na Faransa, Bernard Baudoux, mai shekaru 78, da sanduna.
Jami’an diflomasiyyar daga Faransa, Belgium da Poland, tare da wakilan Cocin Katolika, sun ziyarci wani ƙauye da ke gabashin birnin Ramallah domin nuna goyon baya ga manoman Falasɗinawa.
Ƙauyen na daga cikin yankunan da al’ummomin Kiristoci ke zaune, kuma ziyarar ta gudana ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan hare-haren da ake zargin wasu mazauna matsugunan Isra’ila suna kai wa manoma.
Faransa da Belgium sun yi Allah wadai da harin
Faransa da Belgium sun bayyana harin a matsayin abin takaici, yayin da Belgium ta nemi a ɗauki matakan takunkumi kan Yahudawan masu tsattsauran ra’ayi da ake zargi da hannu a irin waɗannan hare-hare.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ma ta yi Allah wadai da lamarin, tare da jaddada muhimmancin kare jami’an diflomasiyya da tabbatar da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
Isra’ila ta fara bincike kan lamarin
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Sa’ar, ya la’anci harin, amma ya kuma zargi jami’an diflomasiyyar da rashin sanar da jami’an tsaro kafin gudanar da ziyarar.
A nasa ɓangaren, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa ta fara bincike kan lamarin.
Harin ya sake jawo hankalin ƙasashen Turai kan matsalar tsaro a Yammacin Kogin Jordan da kuma buƙatar ɗaukar matakai domin kare fararen hula da jami’an ƙasashen waje a yankunan da ake rikici.
