Kakakin rundunar, Hossein Mohebi, ya ce a lokacin yaƙin da aka shafe kwanaki 40 ana gwabzawa, Iran ta dogara ne galibi da tsofaffin makaman da take da su.

Sai dai ya bayyana cewa tun bayan kawo ƙarshen yaƙin, ƙasar ta samu wasu manyan makamai da suka fi waɗanda take da su a baya ƙarfi.

Duk da wannan ikirari, Mohebi bai bayyana nau’in makaman da Iran ta samu ba, ko kuma inda aka samo su da kuma yadda aka shigo da su ƙasar.

Jami’in na IRGC ya kuma yi gargaɗin cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai ƙarfi ga duk wani sabon hari da aka kai mata.

A cewarsa, Amurka za ta fuskanci mummunan sakamako fiye da wanda ta fuskanta a baya idan ta sake kai wa Iran hari.

Mohebi ya ce: “A wannan karon, sakamakon da Amurka za ta fuskanta zai fi na baya muni.”

Haka kuma, ya yi watsi da ikirarin wasu jami’an Amurka na cewa akwai saɓani da rashin haɗin kai tsakanin shugabannin Iran.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai masu zaman kansu da za su tabbatar da nau’in sabbin makaman da Iran ta ce ta mallaka ba. Haka kuma, ba a bayyana ko waɗannan makaman sun sauya ƙarfin soja na ƙasar ta wace hanya ba.