Babban Sakatare a Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Funso Adebiyi, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara ta duba aikin layin dogon da ya tashi daga Kano zuwa birnin Maraɗi na Jamhuriyar Nijar.
Adebiyi ya ce ma’aikatar tana kuma horar da ma’aikatan jiragen ƙasa kan yadda za su sarrafa sabbin jiragen da kuma kula da su bayan an kawo su ƙasar.
Ya bayyana rashin tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ayyukan sufurin jiragen ƙasa a Najeriya.
A cewarsa, hare-haren da ake kai wa kayayyakin more rayuwa na layin dogo na iya dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa, jefa fasinjoji cikin haɗari da kuma ƙara kuɗaɗen gudanar da ayyuka da gyaran ɓarnar da aka yi.
Rashin tsaro na barazana ga ayyukan layin dogo
Babban sakataren ya ambaci layin dogon Abuja zuwa Kaduna a matsayin misalin hanyar sufurin jiragen ƙasa da ta fuskanci ƙalubalen tsaro.
Ya ce wannan yanayi na nuna muhimmancin ƙarfafa matakan tsaro a dukkan layukan dogo na ƙasar domin kare fasinjoji, ma’aikata da kayayyakin more rayuwa.
Adebiyi ya jaddada cewa kare layin dogo babban abin da ya kamata a ba muhimmanci ne, yayin da gwamnati ke ci gaba da zuba jari wajen faɗaɗa harkokin sufurin jiragen ƙasa da haɗa sassan ƙasar ta hanyar layin dogo.
Sayen ƙarin taragon jiragen ƙasa da na’urorin tsaro na daga cikin matakan da aka bayyana domin ƙarfafa ayyukan sufurin da inganta kariya daga hare-hare.
