A cikin wata sanarwa da mahukuntan kwalejin suka fitar, sun bayyana cewa zargin ba gaskiya ba ne, inda suka jaddada cewa ana gudanar da binciken tsaro ne ga ɗalibai da ma’aikata baki ɗaya domin kare lafiyar al’ummar makarantar.

Sanarwar ta ce ɗalibai mata masu sanya niƙabi ana buƙatarsu ne kawai su bayyana fuskokinsu na ɗan lokaci a wurin binciken tsaro domin tabbatar da asalin mutum, tare da bincikar jakunkunansu kafin a ba su damar shiga harabar makarantar.

Mahukuntan sun ƙara da cewa ba a tilasta wa ɗalibai mata cire niƙabinsu gaba ɗaya ko cin zarafinsu yayin gudanar da binciken tsaron.

Kwalejin ta kuma bayyana cewa babu wata ɗaliba ko ma’aikaciya da aka hana shiga makarantar saboda sanya hijabi ko niƙabi, tana mai zargin cewa wasu daga cikin masu yaɗa jita-jitar na yin hakan ne domin cimma muradunsu na kashin kai da kuma haddasa ruɗani a tsakanin al’ummar Kano.

AKCILS Ta Tuna Da Barazanar Tsaro Ta 2014

A cikin sanarwar, mahukuntan kwalejin sun kuma tuna da wani lamari da ya faru a shekarar 2014, lokacin da jami’an tsaron makarantar suka hana wata mata da suka yi zargin tana da alaƙa da barazanar tsaro shiga harabar kwalejin.

A cewar sanarwar, daga baya matar ta isa ƙofar Kano State Polytechnic, wata makarantar da ke makwabtaka da kwalejin, inda ta tayar da bam.

Mahukuntan sun yi amfani da wannan lamari wajen bayyana muhimmancin matakan binciken tsaro da suke gudanarwa a harabar makarantar.

Sun jaddada cewa manufar matakan ita ce kare ɗalibai da ma’aikata, ba hana mata gudanar da karatunsu saboda sanya hijabi ko niƙabi ba.