Mahukuntan Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa kan wasu ’yan ƙasar biyar da suka ce an same su da laifukan da suka shafi ta’addanci.

A cewar Ma’aikatar Cikin Gida ta Saudiyya, mutanen sun aikata laifuka da suka haɗa da shiga wata ƙungiya ta ƙasashen waje da aka ayyana a matsayin ta’addanci, kai hare-hare kan jami’an tsaro, mallakar makamai da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma tallafa wa hare-hare a cikin ƙasar.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da aka aikata laifukan da aka tuhume su da su ba.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin fargabar tsaro a yankin, musamman bayan hare-haren da ƙungiyar Houthi ta ƙaddamar, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ma’aikatar Cikin Gida ta Saudiyya ta kuma yi gargaɗi cewa duk wanda aka samu da aikata irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Hukuncin ya sake jawo hankali kan yadda Saudiyya ke ɗaukar matakan shari’a kan laifukan da hukumominta ke dangantawa da ta’addanci.