Najeriya na cikin ƙasashe 15 da aka zaɓa domin wakiltar yankunansu a majalisar. Sauran ƙasashen sun haɗa da Brazil, Burundi, Jamhuriyar Dominica, Jamus, Ghana, Ireland, Japan, Jordan, Kuwait, Nepal, Moldova, Ukraine, Uruguay da Zambia.

Zaɓen zai bai wa Najeriya damar shiga tattaunawar ƙasa da ƙasa kan batutuwan kare haƙƙin bil’adama, tare da bayar da gudunmawa wajen tsara manufofi da yanke shawarar da suka shafi wannan fanni.

Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta MDD na da alhakin inganta da kare haƙƙin bil’adama a faɗin duniya. Haka kuma, tana duba matsalolin take haƙƙin bil’adama, bayar da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafi, da sa ido kan yadda ƙasashe ke mutunta haƙƙoƙin bil’adama.

Najeriya ta bayyana cewa zaɓen da aka yi mata alama ce ta amincewar ƙasashen duniya da ƙoƙarin da take yi wajen inganta kare haƙƙin bil’adama.

Ana sa ran Najeriya za ta yi amfani da matsayinta a majalisar wajen ƙara bayar da gudunmawa ga tattaunawar duniya kan kare haƙƙin bil’adama da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe.